An bayyana cewar Najeriya na yin asarar kudin da yakai kimanin Naira Triliyan Biyu da rabi duk shekara ta sanadiyyar cin hanci da rashawa.

Kungiyar kididdiga da kariya daga zamba ta kasa (SFAFP) ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar.

Kungiyar ta bayyana cewar ana samun faruwar hakan ne ta hanyar amfani da kayayyakin gwamnati ta haramtacciyar hanya da kin biyan haraji da kayayyakin da ake shigowa da su.

Kungiyar ta cigaba da cewar sauran hanyoyin sun hada da zamba gami da kwange da biyan albashi ga ma’aikatan bogi, bayar da cin hanci gami da aringizo da sauran badaƙaloli masu yawa.

Shugaban kungiyar Iliyasu Gashinbaki yace kungiyar zata taimaka wajen fallasawa da bankado dukkanin wata badakala da ake amfani dasu wajen ha’intar gwamnati.

Gashinbaki ya kara da cewar cuwa cuwar ba wai kawai a Najeriya ake samun ta ba, ta haka da sauran kasashen nahiyar Afirka.

Ya bayyana cewar a wani bincike da aka gudanar a kwanan nan ya nuna cewa mafiyawan kasashen Afirka na fuskantar matsalolin tabarbarewar arziki da tarin basussuka ne biyo bayan yadda cin hanci da rashawa ke illa ga ‘yan kuɗaɗen da suke samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: