Matashin maai suna Muhammed Obadimeji, ya rasa ransa yayin da yaje yin sulhi a daidai lokacin da Eniyola Ayodele da Kayode Babashola suke faɗa a kan budurwarsu Barakat Wasiu.

Lamarin ya faru ne a yankin Dopemu na birnin Legas.

A daidai lokacin da suke faɗan ne kuma Muhammad Obadimeji ya je don ya rabasu sai Ayodele ya burma masa wuƙa a ƙirjinsa a ƙoƙarinsa na ganin ya sokawa aabokin takarar tasa.

Tuni aka garzaya da Muhammad Obadimeji Babban asibitin koyarwa na jami ar legas.

Jami an ƴan sanda sun kama matasan biyu waɗanda ke faɗa a kan budurwar kuma tuni aka duƙufa don gudanar da bincike ciki har da budurwar da ake faɗa a kanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: