Rundunar ƴan sanda ta cafke direban tare da bincike a kan tuƙin gangancin da yayi sanadiyyar mutum biyu.

Direban mai suna Jamilu Ahmed ya kaɗe wani lauya ne a ƙaramar hkumar Keffi a jihar Nassarawa.
Lauyan da aka gano sunansa Barrister Chiadikoli Ezike da wani mai tuƙin babur sun rasa ransu bayan da wani direban babbar mota ke tuƙin ganganci kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar ASP Ramhan Nansel ya tabbatar da lamarinw anda yace tuni aka kama direban wanda yake tsare a hannunsu.

Ya ƙara da cewa har yanzu suna cigaba da bincike a kan lamarin.