Rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama wata Hauwa u Habibu mai kimanin shekaru 26 bisa zargin kisan gilla da ta yiwa ƴaƴanta biyu.

A ranar asabar ɗin da ta gabata ne jami an ƴan sanda suka samu labarin abinda ya faru wanda ake zargin Habiba ta yi amfani da adda da taɓarya ta sassara ƴaƴanta biyu.


Hauwa u ta Sassari yayanta biyu Irfan mai shekaru 3 da Zuhra mai shekaru 6 kuma sun rasa ransu ƙanwar habiban A’isha mai shekaru 10 wadda ta samu mummunan rauni kuma tuni aka kaita asibitin koyarwa na mallam Aminu Kano don duba lafiyarta.
Kakakin ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace tuni jami ansu suka kamo matar kuma kwamishinan ƴan sandan jihar Habu A. Sani ya bada umarnin miƙa ƙorafin zuwa babban sashen binciken masu muggan laifuka a helkwatar rundunar don gudanar da bincike tare da gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
Lamarin dai ya faru ne a ƴan rariya da ke unguwar ɗisu ƙaramar hukumar gwale a kano.
cikin jawabin da aka tattauna da matar da kuma mijinta, alamu sun nuna cewar ba ta cikin hayyacinta, kasancewar tun a baya ta sha fada masa cewar tana ganin yayan nata suna zuwar mata a wani irin yanayin na daban.
cikin jawabinta ta bayyana cewar akwai rnar da take ganin mijin nata na zuwar mata da kofato.
Shima mijin matar ya bayyana cewar ya fahimci matar tasa na cikin yanayi na firgici, ko da yake ya fada da bakinsa cewa tana yin wasu alamu da yake tabbatar da cewar ba ta hayyacinta.