Kwamishiniyar harkokin mata a jihar Kano Dakta Zahra u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan a jawabinta wajen bikin cikar mujallar shekaru huɗu da kafuwa tare da yaye matasa 200 da aka koyawa sana’o’i kyauta.

Dakta Zahra u Umar ta ce abin farin ciki ne a ga matasa na sana a musamman mata don zamani ya zo da wasu mazan ba sa yin aure sai sun ga mace tana da abin yi.


Ta cigaba da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje za su bada jari, kuma za a zaɓo wasu daga ciki mataan da aka koyawa sana a Mujallar Matashiya don a tallafa musu.
Dakta Zahra u ta ja hankalin matasa maza da mata da su kasance masu kishi da riƙo da abinda aka koya musu don amfanin rayuwarsu.
An yi taron ne a jiya Asabar kuma mutane daban daban ne suka halarci taron.