Rundunar ƴan sandan Kano za ta ƙulla alaƙar aiki mai ƙarfi da Mujallar Matashiya wajen yaɗa manufa da ayyukan rundunar a faɗin duniya.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano Habu Ahmad Sani ne ya bayyana hakan yayin bikin cikar mujallar shekaru huɗu da kafuwa wanda aka yi a jiya.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa DCP Balarabe Sule ƙofar naisa, ya ce rundunar yan sandan Kano ta gamsu da ayyukan mujallar ɗari bisa ɗari wajen yaɗa labarai na gaskiya tare da kawo labarai da shirye shirye don wanzar da zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta zauna da shugabannin mujallar don tsara yadda mujallar za ta zamto kakakin rundunar wajen bayyana ayyuka da manufofinta a fadin duniya.

Rundunar ta kalli ayyukan mujallar kuma ta yaba da irin yadda mujallar ke kawo labaran gaskiya tare da shirye shirye masu amfani ga al umma.

Haka kuma rundunar ta jinjinawa mujallar bisa ƙoƙarin samawa matasa aikin yi don kawar da zaman kashe wando a tsakanin matasan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: