Rundunar ƴan sandan jihar katsina ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a jihar.

An hallaka mutane a garin Diskuru, da Ɗandume bayan ƴan bindigan sun shiga garin.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce, a baya ƴan bindigan sun shiga kuma ƴan garin sukakashe mutane uku daga cikin ƴan bindigan.

Ya ƙara da cewa cikin mutanen da aka kashe akwai ɗan sanda guda ɗaya da jami an sa kai na ƙato da gora.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: