Rundunar ƴan sanda a Kano sun kama wani da ke amfani da sunan fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa Ahmad Musa bisa zargin damfara.

Tun a ranar 25 ga watan Maris ɗin shekarar da muke ciki, rundunar ta samu ƙorafi a kan wanda ake zargi da amfani da sunan ɗan wasan yana damfarar mutane.
Matashin na amfani da sunan fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa kuma yake karɓar kuɗaɗe daga hannun mutane da sunan samar musu dama don buga kwallo a ƙasashen waje.

Bayan samun ƙorafin ne rundunar ta bazama neman Ahmad Musa na boge, kuma an kama shi a ranar 20 ga watan da muke ciki.

Matashin ya damfari mutane sama da goma, wanda kuɗin ya kai sama da naira ubu ɗari bakwai kamar yadda kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Kiyawa ya bayyana.
