Jami’an ƴan sanda a jihar Rivers sun kama wani mai suna Chibueze Ojiriome bisa zargin kashe maƙocin sa.

Chibueze ya hallaka maƙocinsa bayan ya saci akuyar sa kuma ya kashe ta.

Wani da abin ya faru a gaban say a bayyana cewar, sa’insa ta shiga tsakanin mutanen biyu yayin da Chibueze ya nemi akuyar say a rasa.

Tun  a baya Chibueze na zargin maƙocin nasa da sace masa akuyoyi kuma a sandin wannan ya halaka shi.

Lamarin ya faru a Ubinma ta ƙaramar hukumar Ikwerre a jihar.

Jami’an sintiri ne suka fara kama wanda ake zargin daga bisani kuma suka miƙa shi ga jami’an ƴan sanda don faɗaɗa bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: