Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kai hari wani sansanin jami’an tsaro har su ka kashe wasu daga ciki.

Bayan kashe soja guda da wani jami’in hukumar kare fararen hula ƴan bindigan sun sace babura goma tare da ƙona motar sosjoji guda.

Lamarin ya faru ne a Alawwa naƙaramar hukumar shiroro a jihar Neja.

Baya ga harin da su ka kai zuwa sansanin jami’an ƴan bindigan sun kai hari garurwan Gurmana, Bassa, Kokki da Manta duka a ƙaramar hukumar Shiroro.

A jiya Laraba ƴan bindigan su ka sace mutane huɗu a garin Madalla bayan sun kashe wani mai suna Alhaji Sale.

A safiyar yau Alhamis kuwa ƴan bindigan sun kai hari a sansanin jami.an tsaron har su ka sace wasu fafen hula a garin tare da jikkata wasu daga cikin jami’an tsaron.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar ƴan bindigan da su ka kai harin sun haura su 100 sannan kowanne na ɗauke da bindiga ƙirar AK47.

Yayin da jaridar Daily Trust ta tuntuɓi kakakin hukumar ƴan sanda a jihar DSP Wasiu Abiodun bai daga wayar ba har lokacin da aka kammala labarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: