Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta yi nasarar ceto wasu mutane bakwai waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar.

An ceto mutanen ne yayin da aka yi musayar wuta tsakanin jami’an ƴan sandan da ƴan bindigan.
A wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar Bello Kontongs ya fitar, y ace jami’an sun yi aikin ne tare da jami’an sa kai na jihar.

A yayin musayar wutar an kashe ƴan bindiga uku daga ciki.

Sanarwar da aka fitar ranar Litinin ta ce a an kwato tsabar kudi naira dubu ɗari biyu a wata arangama da jami’an ƴan sanda su ka yi da ƴan bindiga a ranar 28 ga watan Afrilun da ya gabata.
Haka kuma a ranar sun kuɓutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Wannan wani mataki ne da kwamishinan ƴan sandan jihar ya dauka domin kakkaɓe ƴan bindigan da ke ɓoye a cikin dazukan jihar.