Rundunar ƴan sanda a jihar Borno sun yi nasarar kubutar da wasu fasinjoji wadanda yan Boko Haram su ka yi yunƙurin sacewa.

Jami’an tsaro ƙarƙashin jagorncin rundunar ƴan sanda sun yi nasarar kubutar da fasinjojin a jiya Juma’a a babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Mayaƙan Boko Haram sun tare babbar hanyar ne dauke da manyan makamai ciki har da motar dauke da bindiga.

A sakamakon haka matafiya da dama su ka tsere zuwa cikin dazuka tare da barin ababen hawan a kan titi.

Ana zargin mayaƙan Boko Haram tsagen Sheƙau ne su ka kai harin.
Wannan ne karo na farko da su ka kai hari bayan tabbatar da mutuwar shugaban nasu Abubakar Sheƙau wanda mayaƙan Boko Haram ɓangaren ISWAP su ka yi.
Jihar Borno helkwata ce da mayaƙan Boko Haram su ka fi addaba a sama da shekaru 10 da fara kai hare-hare.
Bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Sheƙau, wani faifan bidiyo ya bayyana wanda wani sanye da fafafen kaya da baƙin rawani ke kira da marawa sabon shugabancin baya.