Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta bude shafin yanar gizo da ke bayar da dama ga ƴan ƙasar don yin rijistar katin zaɓe.

A yau 28 ga watan Yuni hukumar ta bude shafin bayan kammala tsare-tsaren da aka tanada don yi wa ƴan Najeriya rijista.

Za a yi wa mutanen da suke da shekaru 18 zuwa sama rijistar tare da bayar da dama ga waɗanda katinsu ya lalace ko ya ɓata ko su ka samu sauyin wuri ko unguwar.

Hukumar ta sanya ranar 19 ga watan Yuli domin bai wa ƴan ƙasar damar zuwa wurin da aka ware don yin rijistar domin ƙarasa bayar da bayanansu.

Wannan wani mataki ne da aka ɗauka don tinkarar zaɓen shekarar 2023 a nan gaba.

Kafin samar da manhajar rijistar INEC ta samar da sabbin mazaɓu a wani salon a rage cunkuso a yayin gudanar da zaɓe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: