Babban bankin Najeriya CBN yay i gargaɗi a kan masu wulaƙanta kuɗi da cewar a shirye yak e don gurfanar da su a gaban kotu.

Bankin ya hada kai da jami’an yan sanda da hukumar tattara haraji ta ƙasa da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa don ganin an hukunta mutanen da su ke wulaƙanta kudi.
Bakin y ace hatta masu watsi da kudi a wajen taron bukukuwa ma na daga cikin wadanda su ke karyar dokar cikin sahe na 21(3).

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa wadda daraktan sadarwa na bankin CBN Osita Nwanisobi ya sanyawa hannu a yau Talata.

Bankin y ace ba zai lamunci yadda ake yin watsi da kuɗi a sama lokacin biki da sunan liƙi ba hakan ya saɓa da dokar da a ka yi tanadi tun tuni.
Haka kuma bankin zai kama duk wani da aka samu da karya dokar musamman masu taka kuɗin bayan an yi watsi da su.
Sannan y ace kuɗi alama ce ta alfaharin ƙasa a don haka a ka tanadi doka wadda za ta kare mutuncin sa.