Mutanen wasu ƙauyuka a jihar Neja na tserwa tare da barin muhallinsu don fargabar hare-haren ƴan bindiga.

Mutanen da ke ƙauyukan Karambana, da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja na barin gidajensu don gudun kada yan bindiga su sace su ko su kashe su.
Haka abin yake a ƙaramar hukumar Mariga duka a jihar Neja.

Ƴan bindiga sun mamaye ƙayukan da ke yankunan tare da azabtar da mutane a garin.

Wani mazaunin garin wanda ya kubuta da kyar ya bayyana cewar yan bindigan na azabtar da yara da mata a garin tare da hanasu fita daga ƙauyukan.
Sama da mutane 20 aka kashe a garin Karambana ciki har da kananan yara.
Ƴan bindiga sun mamaye ƙauyukan wana hakan ya jefa mutane cikin firgici da rashin kwanciyar hankali a kowacce rana.
A na zargin akwai ayakan Boko Haram daga cikin wasu da ke addabar jihohin Neja da Sokoto.