Aƙalla mutane shida ne su ka rasa rayukansu a sanadiyyar wani hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Kano.

Hakan ya faru a yammacin ranar Litinin da misalin ƙarfe 6:42 na yamma, kwanaki biyar bayan wani hatsari ya yi silar mutane biyar a Bauchi.
Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a jihar ya tabbatar wa da manema labarai hakan yau a jihar.

Ya ce hakan ya faru ne a sakamakon fashewat tayar mota wandda ke ɗauke da mutane 25 a cikin ta.

Akwai wasu da daga cikin mutanen da abin ya shafa wanda su ka samu munananan raunuka kuma tuni a ka kai su babban asibiti a Bauchi domin kula da lafiyar su.
Ya ƙara da cewa a cikin motar akwai mutane maza da mata sannan wani yaro guda ɗaya.
Tuni su ka miƙa motar zuwa ga ƴan sanda masu lura da zirga-zirgar ababen hawa a jihar domin fadada bincike.
Kwamandan ya yi kira ga jama’a musamman masu tuka ababen hawa da su daina gudun wuce sa’a wanda hakan ke salwantar da rayukan mutane.