Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce a wasu ɓata gari na samar da takardar shaidar allurar rigakafin Korona ta boge a kasar.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaƙi da Korona na fadar shugaban ƙasar Boss Mustapha ne ya bayyana haka a wani taro da ya gudana a Abuja.
Ya ce wasu daga cikin ƴan kasar na samar da takardar gwajin ta boge tare da gargadi a kan masu irin haka da cewar gwamnatin za ta ɗauki mataki a kai.

Boss Mustapha ya ce gwamnatin na shirin kammala wa kashi 50 na ƴan ƙasar allurar rigakafin Korona zuwa ƙarshen watan Janairun 2022.

Ya ƙara da cewa akwai wani gangami da za a yi don ganin an yawaita yin allurar ga yan ƙasar domin cimma tsarin ta na yi wa kashi 50 na yan ƙasar.
Za a fara gangamin ne daga 20 ga wtaan Nuwamban da mu ke ciki.
Boss Mustapha ya ce gwamnatin ƙasar ta tabbatar da samun saukin yaɗuwar cutar sai dai hakan ba zai hana ta ci gaba da ɗaukar matakan kare al’umma ba.