Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta yi gargaɗin ɗaukar mataki muddin gwamnati ba ta mutunta yarjejeniyar su ba.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya sanar da haka a yayin tattaunawarsa da jaridar Daily Trust.
Ya ce za su gudanar da wani gagarumin zama da sauran mambobin ƙungiyar da ke sassa daban-daban na ƙasar kafin yanke hukunci a kan matakin da za su ɗauka a gaba.

Ya ƙara da cikin matakin da za su ɗauka zai zo ne ƙasa da sa’o’i 48 a nan gaba.

Tun a baya ƙungiyar ta yi barazanar shiga yajin aiki wanda barazanar ta sa ɓangaren gwamnatin Najeriya su ka nemi zama da su.
Sau da dama ƙungiyar na tafiya yajin aiki a ƙasar a bisa rashin mutunta yarjejeniyar su da ɓangaren gwamnatin Najeriya.
Tafiya yajin aikin malaman jami’o’i a Najeriya na haifar da koma baya ga karatun ɗaliban jami’o’i a ƙasar.