Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da manyan shugabannin tsaro karƙashin jagorancin mai ba shi shawara a kan tsaro Babagana Munguno don jajanta wa al’ummar Sokoto da Katsina.

Shugaban ya aike da wakilcin kwana guda da kashe kwamishina a jihar Katsina.
An hallaka jama’a matafiya a Sokoto waɗanda aka kone suda ransu a cikin wata mota.

Jama’ar Najeriya na ta bayyana ra’ayinsu a kan yadda shugaban ke ware yan arewacin kasar da nuna halin ko in kula a kan yanayin da su ke ciki.

Shugaba Buhari ya ziyarci jihar Legas don bude wasu ayyuka da kuma ƙaddamar da littafi a ranar Alhamis.