Hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa arewa ne ya sa shugaban ba ya zuwa jaje arewa a cewar minsitan harkokin ƴan sandan Najeriya.

Minsitan harkokin ƴan sanda a Najeriya Muhammad Mai Gari ya bayyana cewar rashin tsaron da ya yi ƙamari a arewa ne ya hana shugaba Buhari zuwa jaje jihohin da ake fama da rashin tsaro.

Maigari ya bayyana haka ne yayin ganawar sa da BBC a kan yadda ake sukar shugaban kan rashin zuwa don jajanta wa a kan al’amuran da su ka faru a Sokoto.

Ya ce yawiatar hare-haren ƴan bindiga ne ya hana shugaban zuwa ziyarar jaje jihar.

Ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa a arewa na da yawa kuma babu damar da shugaban zai iya zuwa da kansa duk wuraren da ake kai hare-haren.

Ministan y ace idan shugaban ya aike da wakilci tamkar ya je ne don haka ba lallai ne sai shugaban ya je da kan sa ba.

Mutane na sukar yadda shugaban ke nuna wariya da fifita yan kudancin ƙasar a kan abubuwan da su ka shafe su duk da cewar ana kai munanan hare-hare arewacin ƙasar.

Shugaban ya je wata ziyara jihar Legas tare da shan alwashin zaƙulo waɗanda su ka kashe wani yaro a jihar.

Sai dai mutane na kallon hakan a matsayin nuna halin ko in kula da yankin arewa da ake kashe ɗaruruwan mutane da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: