Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce mutane 1,547 ne su ka kamu da cutar Korona a ƙasar ranar Lahadi.

Babban birnin tarayya Abuja ne ke da adadi mafi yawa na mutanen da cutar ta kama a ranar Lahadi.

A sanarwar da hukumar ta fitar a daren Lahadi, hukumar ta ce mutane 3022 cutar ta hallaka zuwa yanzu.

Hukumar ta ce an samu masu cutar a jihohin Legas, Borno, Oyo, Osun, Ogun, Kano, Katsina, Jigawa, da kuma jihar Ekiti.

A halin yanzu akwai jimillar mutane 237,561 waɗanda aka tabbatar cutar ta taɓa kama wa a Najeriya, sai dai an sllami fiye da kashi 70 cikin 100 na wadanda cutar ta kama.

Cutar ta ci gaba da bazuwa a ƴan kwanakin nan, tun bayan da aka tabbatar da ɓullar sabon nau’in cutar na Omicron.

Gwamnatin ƙasar na ci gaba da kira ga al’ummar ta da su ci gaba da bin matakan kariya domin kare kansu daga kamuwa da cutar tare da hana yaɗuwar ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: