Haɗaɗɗiyar daular larabawa sun ɗage takunkumin da aka sanya wa wasu kasashen Afrika a bisa zargin ɓullar sabon nau’in Korona na Omicron.

Hukumomi a haɗaɗɗiyar daular ne su ka sanar da hakan waɗanda su ka janye takunkumin daga ƙasashe 12 na Afrika ciki har da Najeriya.

Yankin sun dakatar da jigilar mutane daga yankin Afrika don gudun yaduwar sabon nau’in Omicron na Korona.

Ƙasashen da aka ɗage wa takunkumin sun haɗa da Botswana, Mozambuque, Afrika ta kudu, Tanzania, Zimbabwe, Kenya da ƙasar Ehtiopia.

Sauran su ne Congo, Eswatini, Lesotso, Namibia da ƙasar Najeriya.

Yankin ya sanar da cewar za a iya fara jigilar mutane zuwa yankin daga ranar Asabar mai zuwa.

ɓullar annobar Korona ya dakatar da al’amura a mafi yawan ƙasashen duniya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: