Hukumomi a kasar saudiyya sun ɗage haramcin da aka sanya wa Naajeriya da wasu ƙasashwn Afrika.

Sanarwar da hukumomin au ka fitar a yau, sun janye haramcin shiga ƙasar wanda au ka sanyawa ƙasashen Najeriya, Afrika Ta Kudu, Botswana, Madagascar, Zimbabwe, Ethiopia, Lesotho, da sauransu.

An sanya wa ƙasashen haramcin shiga saudiyya ne domin zargin ɓullar sabon nau’in Korona samfurin Omicron.

Saudiyya na ɗaukar matakai masu tsauri a kan cutar Korona la’akari da yadda aka dakatar da gudanar da ibaada a cikin cunkuso da kuma takaita mutane masu shiga masallatan harami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: