Aƙalla mutane biyar ne su ka mutu a yayin da ƙasa ta rufta musu lokacin da su ke haƙar ta don yin gini.

Mutane biyar ɗin mazauna ƙauyen Ƴn Lami a ƙaramar hukumar Bichi sun gamu da ajalinsu a a ranar Asabar ɗin ƙarshen makon da ya gabata.
Mutanen da su ka mutu sun haɗa da Muhammad Sulaiman mai shekaru 35, da Jibril Musa mai shekaru 30, sai Masa’udu Nsiru mai shekaru 25 sannan Jafaru Abdulwahab mai shekaru 30 sai kuma Alasan Abdulhamid mai shekaru 22 a duniya.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara a jihar Kano SFS Saminu Yusif Abdullahi ya ce matasan sun tafi haƙar ƙasar ne domin gina wa abokinsu gida wanda ya ke gab da angwancewa.

Ya ce jami’an su sun isa wurin bayan karɓar kisan waya daga wani Malam Sanusi Badume a ranar Asabar.
Tuni hukumar ta miƙa gawarwakin mutanen ga dagacin Yan Lami a ƙaramar hukumar Bichi domin yin jana’izarsu kamar yadda addini ya tanada.
