Daga Khadija Ahmad Tahir

‘Yan bindigan sun kai harin ne a safiyar Alhamis a unguwar galadima da ke cikin karamar hukumar Gonin Gora a karamar hukumar Chikun ta Jihar ta Kaduna.
Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN reshen Jihar Kaduna shine wanda ya bayyana faruwal Lamarin inda ya ce ‘yan bindigan sun kusa kai awa guda su na cikin garin.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa zuwan su ke da yuwa su fara jiyo karar harbe-harbe ‘yan bindigan akan al’ummar garin.

Har ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sandan Jihar ba ta ce komai ba dangane da faruwal harin da ‘yan bindigan su ka kai a yau.
Jihar Kaduna na fama da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga wanda hakan ya ke sanya tsoro a zukatan mutanen yankunan da ‘yan bindigan su ke kai musu hare-hare