Shugaban ƙungiyar yan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo Hisham Habib ne ya bayyana haka a yayin ganawa da mambobin ƙungiyar yau Asabar.

Hisham Habib ya hori mambobin ƙungiyar da su ƙauracewa labaran ƙarya tare da daƙile hanyoyin yaɗuwarsa a yanar gizo.
Shugaban ya ce wajibi ne su tashi tsaye domin kawo karshen labaran ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sadarwa.

Sannan ya umarci mambobin ƙungiyar da kada su yarda a yi amfani da su don amfanin wani bangare a siyasa musamman abin da ba su da sahihancinsa.

An gudanar da taron a yau Asabar kuma da yawa daga cikin mambobi da shugabannin ƙungiyar sun halarta.