Yayin da hukumar ta mayar da hankali don ganin yan jihar Kano sun mallaki katin zaɓe na din-din-din, hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano za ta fara zagaye domin tabbatar da cewar ta yi wa mutanen jihar rijista musamman waɗanda shekarunsu ya kai 18 zuwa sama kuma basu da rijistar.

Hukumar ta dauki matakin haka ne domin tabbatar da cewar an yi wa mutanen da su ka cancanta rijista tare da saukakawa jama’a.
INEC ta dauki matakin haka ne domin tabbatar da cewar an bai wa kowa haƙƙinsa na ganin ya sami damar yin rijistar kamar yadda doma ta bayar da dama.

Hukuma ta sanya ranar Litinin 14 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki a matsayin ranar da za ta fara gudanar da zagayen a mazaɓu 484 na kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Sannan za a kammala a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar da mu ke ciki.
Hukumar zabe ta INEC a Kano ta ce zagayen ba zai shafi aikin gudanar da rijistar a helkwatar hukumar ba da kuma ofisoshin hukumar na kananan hukumomi.