Rundunar tsaron hadin gwiwa a Najeriya ta ce ta samu nasarar hallaka ƴan bindiga sama da ɗari a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Jami’an tsaron hadin gwiwa tsakanin sojoji da ƴan sanda da kuma ƴan banga sun kai farmaki yayin dayan bindigan su ka yi yunƙurin kai hari a Bangi ƙaramar hukumar Mariga ta jihar.

Al’amarin ya faru a ranar Laraba da misalin ƙarfe 6:00pm na yamma yayin da ƴan bindohga su ka kai hari garin, sai dai jami’an tsaron sun sami nasarar hallaka da yawa daga cikinsu.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da al’amuran staron cikin gida Emmaunel Umar ya tabbatar da cewar sama da ƴan bindiga 100 nesu ka rasa rayukansu a yayin da jami’an su ka daƙile harin.

Ya ƙara da cewa jami’an sun samu nasarar ƙato babura 50 yayin da su ka yi musayar wuta da ƴan bindigan.

Kwamishinan ya ce a ranar Talata ƴan bindigan sun kai hari yankin Nasco tare da kashe wani baturen ƴan sanda da kuma wasu jami’an tsaro kuma daga bisani su ka kai hari Bangi a ranar Laraba wanda aka samu nasarar daƙile harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: