Wata babbar kotu a jihar Legas ta wake wata mai suna Mary Alilu bayan an zarge ta da hallaka mijinta.

Gwamnatin jihar ce ta gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu tun a ranar 12 ga watan Nuwamba na shekarar 2018.
Tun da farko, an zargi Mary Alilu da yanke kan mijinta wanda hakan ya yi silar mutuwarsa.

Alƙaliyar kotun Justice Modupe Nicol-Clay ya wanke wadda ake zargin a zaman kotun.

Wadda ake zargi ta kare kanta a gaban kotun tare da gabatar da shaidu guda biyu.
Alƙaliyar kotun tta ce an gabatarwa da kotun ƙunshin tuhumar da ake yi wa Mary tare da bayar da labarin cewar ana zargin ta hallaka mijin nata da wuƙa sai dai ba a gabatar da wuƙar a gaban kotu ba.
Sannan kotu ba ta sami wasu hujjoji da su ke tabbatar da zargin da ake yi wa matar ba, a don haka kotun ta wanke wadda ake zargin.