Kimanin mutane 50 ne su ka rasa rayukansu yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama a wani harin ƴan bindiga da su ka kai ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Lamarin na baya-bayan nan ya zo ne mako guda bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 37 a wani hari makamancin haka a masarautar Agban Kagoro da ke karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.
Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun ce su na ci gaba da gudanar da bincike kan sabon harin tare da tattara hakikanin adadin wadanda suka mutu.

Sai dai wani shugaban a karamar hukumar Giwa Musa Ahmed ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan ta’addan sun kai hari kauyuka shida tsakanin daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a.

‘Yan bindigar sun mamaye garurwan inda suka bude wuta kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Dillalai, Barebari, Dokan Alhaji Ya’u, Durumi, Kaya, da Fatika, yayin da maharan suka kona gidaje da babura da dama sannan su ka kuma yi awon gaba da shanu sama da 100 na mutanen yankin.