Rundunar sojin Najeriya ta gano wani jirginta da ya ɓace a cikin dajin sambisa n ajihar Borno.

Rundunar sojin ta gano jirgin bayan watanni 11 da su ka gabata wanda jirgin ya ɓace a ranar 31 ga watan Maris ɗin shekarar 2021.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar yau Asabar ta ce ta gano jirgin a dagargaje alamun an baro shi ne daga sama.

Sai dai ta ce mutane biyu ne a cikin jirgin yayin da ya ɓace.

Jirgin mai lamba NAF475 na aikin tsaro ƙarƙashin dakarunta na Operation Desert Sanity da ke aikin samar da tsaro tare da kakkaɓe mayaƙan Boko Haram.
Rundunar ta ce ta na kan gudanar da bincike a dangane da ɓurɓushin jirgin da ta gano, kuma za su bayar da cikakken bayani bayan sun kammala bincike.