Gwamnatin tayarayyar Najeriya ta yi zargi wasu da haɗa fitina wajen saka haddasa zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Minsitan yada labarai da al’adu a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja.
Ya ce ƴan jam’iyyar adawa na ƙoƙarin haddasa mummunar zanga-zanga a fadin ƙasar domin kassara mulkin shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari.

Lai Mohammed ya yi zargin cewar yan jam’iyyar adawar na shirya maƙarƙashiyar haka ne bayan da jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta na ƙasa wanda hakan ke nuna smaun nasararta a gaba.

Ya ce waɗanda su ke ƙoƙarin shirya zanga-zangar na yi ne domin dakushe nasarorin da gwamnatin su ta samar daga lokacin da ta fara shugabanci zuwa yanzu.
Sannan ya ja hankalin masu yin hakan da su farga a kan cewar hakan na iya tarwatsa ƙasar kuma babu wani waje da za su je wanda ya kai Najeriya.