Hukumar hana cunkoson ababen hawa a jihar Kano Karota za ta ci gaba da kama masu adaidaita sahun da ba su rubuta koriyar lamba baro-ɓaro a jiki ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukuma Nabilusi Abubakar ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau Litinin.
Ya ce hukumar ta lura cewar akwai adaidaita sahu da dama da ba a rubuta koriyar lamba a jiki ba a don haka za ta ci gaba da kama wadanda su ka karya dokar.

A cewar sanarwar da kakakin ya fitar, wasu ƴan kishin jihar Kano ne su ka ankarar da hukumar a kan wasu babura da ake haya da su ba tare da an rubuta lambar a jiki ba.

Sannan ya ce hukumar a shirye ta ke domin ganin ta karɓi shawara ko korafi a kan dukkanin wani abu da mutane ba su gamsu da shi ba.
Idan ba a manta ba, a watan Disamban shekarar da ta gabata matuka baburan adaidaita sahu su ka tafi yajin aiki a dangane da kuɗin harajin da hukumar ke karba daga wajensu, sai dai daga bisani an daidaita bayan da wasu daga cikin ƙungiyoyi da ɓangaren gwamnati su ka shiga tsakani.