Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu ta na ci gaba da aiki tuƙuru domin tabbatar da cewar ta ciƙa manufofin ta na samar da aikin yi, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma samar da tsaro da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayayna haka a ranar Asabar yayin da jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta na ƙasa.

Ya ce jam’iyyar APC ta mayar da hankali ne domin ganin an kawo ƙarshen dukkan matsalolin da Najeriya ke fuskanta tare da tabbatar da ita a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya.

Osinbajo ya ƙara da cewa an samar da aikin yi da yawa a tsakanin ƴan ƙasar wanda hakan ya yi silar fitar da miliyoyin  utane daga ƙangin talauci.

Ya ce mutane miliyan 100 ne su ka fita daga ƙangin talauci a gwamnatin shugaban Njeiya Muhammadu Buhari.

Sannan ya yi kira ga sabbin shugabannin jam’iyyar APC da aka zaba da su taimaka wajen cimma manufofin shugaban Najeriya na yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da tsaro musamman a watannin da su ka rage masa na mulkin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: