Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka ƴan bindiga fiye da 30 a wasu hare-hare da su ka kai musu ta sama a Kaduna.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta hallaka ƴan bindigan ne a tsakanin Sarkin Pawa hanyar da ta haɗa tsakanin Kaduna da jihar Neja.
A cewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar, ta ce sun sami bayanai a kan ƴan bindigan na kan babura kuma su na kan hanyarsu ta zuwa Sarkin Pawa daga garin Aƙibu.

Rundunar ta ce ta yi amfani da jiragen yaƙi wajen hallaka ƴan bindigan da su ka kai 40.

Sannan an ga bindigu ƙirar AK47 guda 14 da baburan hawa guda 17 sai kuma gawar wɗanda ake kyauta zaton ƴan bindiga ne guda 34.
Harin a jami’an sojin su ka kai ya zo ne ranar Laraba yayin da ake jimami a kan mummunan harin da ƴan bindiga su ka kai hanyar jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.