A yau Asabar mafi yawan ƙasahsn musulmi sun fara azumtar watan Ramadan bayan an tabbatar da ganin wata a wasu daga cikin ƙasashen duniya.

Ƙasar Saudiyya ta tabbatar da ganin watan a ranar Juma’a yayin da aka ga watan a ƙashe kamar Najeriya, Nijar, Benin da sauran ƙasashe.

Wataran Ramadan wata ne da musulmi ke ruɓanya ayyukan da su ke ƙara kussantar su ga Allah S.W.A.

Malam Hamza Bin Ishaƙ babban limamin masallacin Juma’a na Ɗantamashe a Kano ya bayyana mana wasu ayyuka da ya kamata mai azumi ya dinga yi domin ƙarin samun lada a wajen Allah.

Malam Hamza Ishaƙ ya ce ana son mai azumi ya kasance ya kiyaye ganinsa, jin sa da kuma kaicewar dukkanin wani zamce da ba na alhweri ba.

Sannan ya ce ana son mutane su kasance masu kyautatawa masu azumi ta hanyar ciyarwa komai ƙanƙantar abin da mutum ya mallaka.

Watan azumin Ramadan na iya yuwuwa ya kasnace kwanaki 29 ko 30 daga nan kuma ake gudanar da idin karamar sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: