Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar.

Sanarwar hakan ta fito daga ofishin ministan harkokin cikin gida Ra’uf Aregbesol.

An ayyana ranakun a matsayin ranar hutu domin zagayowar ranar Easter da aka saba duk shekara.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun babban sakatare a ma’aikatar Dr. Shu’aib Belgore, anarwar ta umarci mabiya addinin kirista na ƙasar da su kasance masu haƙuri, yafiya da kuma sadaukarwa.

Sanarwar ta ƙara da cewar gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da mayar da hankali wajen tabbatar da cewar ansamar da zaman lafiya tare da kawo ƙarshen tashe-tahen hankula da ake fama da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: