Hukumar ƙidaya a Najeriya (NPC) ta amince da sake ƙidayar yan ƙasar a watan Afrilun shekarar 2023.

Wannan ke nuni da cewar za a gudanar da ƙidayar ƴan Najeriya bayan gudanar da zaɓen shekarar 2023 da ake tunkara a gaba.

Shugaban hukumar Nasire Isa ne ya shaida haka jim kaɗan bayan kammala taron majalisar tsaffin shugannin Najeriya wanda ya gudana yau a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ya ce za su fara shirye-shiryensu daga watan Yunin shekarar 2022 da mu ke ciki bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyun ƙasar.

A wannan karon hukumar ta ce za ta yi amfani da matuƙar fasahar zamani wajen gudanar da aikin ƙidayar yan Najeriya.

Ya ƙara da cewa  ta hanyar ƙidaya ne za a iya samar datare-tsaren da za su dace da yan ƙasar wanda hakan zai taimaka tare da kawo ci gaba.

Idan za a iya tunawa an yi kidayar ƴan ajeriya tun a shekarar 2006 kuma daga wannan ba a sake yi ba sai a wannan lokaci da aka stara gudanarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: