Wani malamin makarantar gaba da firamare mai suna Malam Buhari Ibrahim yayi kira ga iyaye da su bar ‘yayan su mata su shiga harkar siyasa don kawo cigaba mai ma’ana.

Malam Buhari ya bayyana haka ne a yau Asabar wanda ya ce akwai buƙatar mata su sake nitsawa cikin harkokin siyasar kasar nan.

Ya ce akwai gudunmawar da mata za su bayar a harkokin siyasa domin samar da cigaba a cikin al’umma.

Wannan kira nasa ya biyo bayan Daya daga cikin daliban sa da ta nuna sha’awarta na tsayawa takarar Majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Nassarawa da ke birnin Kano.

Ƴar takarar mai suna Khairat Imam Auta wadda tuni sunan ta ya watsu a shafukan sa da zumunta wadda ta kasance matashiya mai ƙananan shekaru dalibace ga malamin, inda ya nuna jin dadinsa da kuma goyon baya tare da yi mata addu’ar fatan samun nasara.

A karshe ya yi kira ga takwarorin ta da su fito a dama da su a harkokin siyasa don su cike guraben da tsarin Mulki ya tanadar musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: