Aƙalla yara shida aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon ɓarin wutar da wani jirgin sojin saman Najeriya ya yi a yankin Kuregba na jihr Neja.

Jirgin ya yi sanadiyyar rasa rayuwar yara shida yan tsakanin shekaru biyar zuwa 12 a Kuregba da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Jirgin sojin samn na aikin kawar da ƴan bindga ne a ƙoƙarinsa na tarwatsa su sai aka sami akasi ya yi luguden wutar a kan ƙananan yaran.

Mazauna yankin sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewar irgin ya lalata gidaje da dama yayin da al’amarin ya faru a ranar Laraba.

Wani shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyoyin a Shiroro ya ce lamarin ya rutsa a yaran yayin da su ka tafi diban ruw a wani famfon tuƙa-tuƙa.
Ya ƙara da cewar wajen da jirgin sojin saman ya kai hari ba maɓoyar yan bindiga ba ne lamarin da ya rutsa da yaran su shida su ka rasa ransu.
Rundunar sojin saman Najeriya ba ta ce komai a dangane da lamarn ba har wannan lokaci da mu ke kammala labarin.