Kakakin hukumar ne ya bayyana haka yau Litinin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Ya ce an kama matasan su takwas su na shaye-shaye da tsakar rana yayin da musulmi ke gudanar da ibadar azumin Ramadan.

A na zargin matasan da yin kwacen waya yayin sallolin dare da ake yi a masallatan da ke kusa.

Tuni aka kai matasan helkwatar hukumar da ke unguwar sharaɗa tare da gabatar da su a gaban babban kwamamdan hukumar.

Kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya ja hankalin mutanen da aka kama da su tuba tare da komawa ga Allah a kan abin da su ke yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: