Ahmad Sulaiman Abdullahi

Shugaban hukumar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa (rtd) ya rubuta wasiƙa ga shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu, inda ya buƙaci a baiwa jami’an NDLEA damar gudanar da gwajin tabbacin kuɓuta daga shan kwaya ga ƴan siyasa da ke neman takara.

Marwa ya ce a lokacin da PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zaɓukan fidda gwani, zai kuma rubuta musu wannan buƙata ta gwajin.

Shugaban na NDLEA wanda ya yi jawabi a wajen bikin karramawar kwata-kwata na farko a 2022 na hukumar a Abuja.

Ya bayyana cewa gwajin shan kwaya ya zama dole don tabbatarwa da samar da ƴan siyasa masu muhimmanci ofisoshin gwamnatin kasar nan.

Ya bayyana cewa, dabarar hakan shi ne a dakile ƴan siyasa daga amfani da kason kasafin kuɗi wajen sayen hodar iblis ko maganin Methamphetamine maimakon samar da ayyukan da suka cancanta ga talakawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: