Mataimakin shugaban kasa Muhammad Buhari Farfesa Yemi Osinbanjo ya bayyana cewa matukar bai tsaya takarar shugabanci Najeriya ba a shekarar 2023 to tabbas yaci amanar ‘yan Najeriya.
Osinbanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci gwamnan Jihar Ondo a jiya Litinin tare da wasu manya a jam’iyyar su ta APC.
Yemi ya ce tun daga lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasa ya samu kwarewa sosai ta yadda zai iya mulkar kasar Najeriya.
Osinbajo ya kara da cewa matukar bai nemi kujerar shugaban kasa Muhammad Buhari ba to yaci amanar matanen Najeriya musamman ma yawan kashe-kashen mutanen da ake yi a fadin Najeriya.
Tun bayan bayyana kudurinsa na tsayawa takara Osinbanjo ya ke ziyartar gurare daban-daban domin neman yarda da goyan baya domin ya ga ya tabbatar da gudurinsa na darewa kan kujerar shugabancin Najeriya.


