Majalisar dokokin Najeriya ta zartar da doka a kan masu biyan kuɗin fansa don ganin sun fuskanci ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

Ƙudirin dokar da aka gabatar tare da zartar da shi a zauren majalisar ya ƙunshi ɗaurin rai da rai ko hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da aikata satar mutane.
Tun a baya dai aka gabatar da ƙudirin haramta biyan kuɗin fansa daga ƴan uwan wɗanda aka sace yayin da majalisar ta yi dokar ɗaurin shekaru 15 ga duk wanda ya biya yan bindiga kuɗin fansa.

Majalisar ta ce haramta biyan kunɗin fansa ga yan bindiga zai taimaka wajen rage yawan satar mutane a da ake fama da shi a ƙasar.

A bisa nazarin da majalisar ta yi ta gano cewar biyan kudin fansar da ake yi shi ke ƙara ta’azzara satar mutane a ƙasar.
Bayan majalisar ta gama muhawara a kan dokar za a aike da ita gaban shugaban ƙasa domin sanya hannu a kan ta.
Mutane a Najeriya na cece-ku-ce a kan dokar ɗaurin shekaru 15 ga wanda aka samu ya biya kuɗin fansa a bayan sace ɗan uwansa.