Jam’iyyar PDP a Najeriya  ta haramtawa wasu ƴan takarar shugaban ƙasa guda biyu tsayawa takara bayan tantance su.

A daidai lokacin da ake siyan fom ɗin takara a jam’iyyar domin tunkarar zaɓen shekarar 2023.

Jam’iyyar PDP ta hamtawa biyu daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa daga cikin ƴan takara 17 da su ka nuna sha’awar tsayawa.

Shugaban kwamitin tantance ƴan takarar David Mark bai sanar da sunayen mutanen da aka hana tsayawa takarar ba.

Amma jam;iyyar ta tantance wasu daga cikin ƴan takarar da su ka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Sanata Bukola Saraki da gwamNAN Sokoto Aminu Waziri Tambuwa.

Sauran ƴan takarar da aka tantance sun haɗa da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da Peter Obi sai Pius Anyim.

Babbar jam’iyyar adawa da PDP na sukar tsarin jam’iyya mai muulki, ko da a kwanan nan sai da ta soki batun kuɗin fom ɗin takara da jam’iyyar APC ta sanar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: