Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar nan da wani kanƙanin lokaci za a ƙarasa murƙushe mayaƙan Boko Haram a Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a saƙon da ya aikewa ƴan Najeriya yayin da ake bikin idin ƙaramar sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.
Shugaba Buhari ya ce an kusa ƙarasa murƙushe mayaƙan Boko Haram masu fakewa da addini su na ta’addanci.

Sannan ya za a tabbatar ba a samu ƙarancin kudi ba a gwamnatinsa, sannan za a ci gaba da inganta tsaro domin samun zaman lafiya.

Lokaci zuwa lokaci gwamnatin na bayyana cewar za ta kawo karshen matsalar tsaron da ake fuskanta musamman a gabashin ƙasar wajen da mayaƙan Boko Haram su ka fi ƙarfi.
Yaƙi da Boko Haram tare da kwar da cin hanci da rashawa na daga cikin manufofin da shugaba Muhammadu Buhari ya yaɗa yayin yaƙin neman zaɓen sa a shekarar 2015.