Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar lll ya buƙaci ƴan siyasa a Najeriya da su bayar da hadin kai domin wanzuwar zaman lafiya.

Sarkin musulmi ya bayyana haka ne a saƙon taya murnar idin ƙaramar salla wanda ya aikewa al’ummar Najeriya.
Sarkin musulmi ya buƙaci ƴan siyasa da kada su bari wani masoyinsu ya yi amfani da damarsa wajen rusa zaman lafiya da kwanciyar hakali a ƙasa.

Ya ce a wannan lokaci da ake tunkarar zaɓen shekarar 2023 ya na da kyau a mayar da hankali wajen zaman lafiya sannan babu wani zaɓi da ya wuce zaɓin Allah.

Sannan ya buƙaci al’ummar musulmi da su ci gaba da godiya ga Allah da ya sanya aka azumci wata mai falala watan Ramadan.
Ya ce wannan babbar dama ce da Allah ya bai wa mutane wajen ganin sun zauna lafiya musamman idan aka riƙe addu’o’i da godiya ga Allah S.W.A.