A sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta tsawaita a yau Litinin, dalibai da dama ne a Jihar Legas su ka tsunduma zanga-zanga domin yajin aikin da kungiyar ta ASUU ta tsawaita.

Daliban na UNILAG dai na neman gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan da kungiyar ta ASUU a yau Litinin ta kara tsawaita yajin aikin da ta ke yi zuwa watan August.

Wanda hakan ya sanya daliban su ka fito manyan tituna domin kin amincewar su da tsawaita yajin aikin,inda su ka nemi da gwamnatin tarayya da ta yi duba ga kungiyar ta ASUU.

A yayin zanga-zangar ta daliban sun fito ne dauke da alluna masu madauke da rubuce-rubuce wanda ke nuna kin amincewa, wanda hakan ya sanya fannin ilmin ya tabarbare a Najeriya.

Daliban sun kuma bayyanawa gwamnatin cewa matukar ba ta kawo karshen yajin aikin ba to babu shakka za su rufe manyan tituna.

 

Daliban jami’o’i a fadin Najeriya na kokawa akan yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi wanda hakan ya kawo koma baya a karatunna su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: