Gwamnatin Jihar Sokoto ta saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar.

Gwamnatin ta sanya dokar sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka gudanar a yau Asabar.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce dokar za ta fara aiki nan take.

Gwamnatin ta bayyana ɗaukar matakin ne “saboda dawo da doka da oda a birnin Sokoto da jihar baki ɗaya”, a cewar sanarwar.

Cikin rahotan da muka wallafa dazu kunji cewa masu zanga-zangar na neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ake zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).