Ƙungiyar gwamnonin ta Arewaci, ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankali tare da rungumar zaman lafiya biyo bayan zanga-zangar kisan matashiyar da ake zargi da zagin Manzon (S.A.W) a Sokoto.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Filato Simon Lalong ya ce, ƙungiyar ta shiga damuwa kan halin da Sokoto ta shiga.
Gwamna ya ce, “Gwamnonin Arewa sun damu da abin da ke faruwa, wanda lamari ne da ya saɓa wa shari’a ta fuskar ɗaukar doka a hannu”.

“Don haka gwamnonin na kira da a zauna lafiya bayan rahotannin rikiɗewar zanga-zangar lumana zuwa rikicin da ya janyo sanya dokar hana fita.”

Kazalika, gwamnonin sun ce duk wani yunƙuri na ɗaukar doka a hannu – kan lamarin addini ko akasin haka – “zai iya tayar da ƙarin rikici”.